Wani soja ya fado daga jirgi mai saukar ungulu a Belgium

Dakaru na can suna neman gawar wani matukin jirgin soja a gabashin Belgium bayan ya fadi daga cikin jirgi mai sukar ungulu a lokacin atisayen sojin sama.

Wani soja ya fado daga jirgi mai saukar ungulu a Belgium

Dakaru uku sun dira daga jirgin samfurin Agusta A-109 da taimakon lema, ko da yake da matukin jirgin da mataimakinsa ba su da lema, in ji kafafen watsa labaran kasar. Sun ce daya daga cikin matuka jirgin ya taimaka wa mutum uku yin tsalle suka fice daga cikinsa, kuma daga bisani sun ga babu kowa […]

Gurbataccen Kwai ya fara isa Asiya daga Turai

Badakalar gurbataccen kwan ta haddasa taya da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen Turai

Gurbataccen Kwai ya fara isa Asiya daga Turai

Badakalar yaduwar gurbataccen kwai da ta mamaye kasashen Turai 15, ta fara shafar nahiyar Asia, in da a baya-bayan nan matsalar ta isa Hong Kong. Ministocin kasashen Turai da manyan jami’an kula da lafiyar abinci, za su gudanar da taro a ranar 26 ga watan Satumba, a wani yunkuri na kawo karshen zarge-zargen da kasashen […]

‘Yan Sandan Spain Sun Kashe Maharin Barcelona

Jami’an ‘Yan sandan Spain sun halaka Younes Abouyaaqoub da ake zargi da kai harin Bercelona da ya kashe mutane 16 tare da jikkata sama da 100, akasarinsu ‘yan kasashen ketare.

‘Yan Sandan Spain Sun Kashe Maharin Barcelona

Jami’an ‘Yan sandan sun harbe Abouyaaqoub mai shekaru 22 har lahira a yankin Sabirat mai nisan kilomita 60 daga Bercelona, lokacin da ya ke kokarin ficewa daga birnin. A safiyar yau ne dai gwamnatin Spaniya ta sanar da kammala gano dukkanin mutane 16 da harin na Bercelona ya ritsa da su, ciki har da ‘yan […]