Za a Rataye Sojan Nigeria Kan Kisan Abokiyar Aikinsa

Kotun rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yanke wa wani jami'inta hukunci kisa ta hanyar ratayewa, sakamakon kashe wata abokiyar aikinsa da ya yi.

Za a Rataye Sojan Nigeria Kan Kisan Abokiyar Aikinsa

ACM Bernard Kalu ya harbe abokiyar aikinsa ACW Sholape Oladipupo a watan Maris a sansanin sojin sama da ke birnin Makurdi a jihar Benue. Da yake yanke hukunci kan shari’ar a ranar Talata, alkalin kotun Group Captain Elisha Bindul, ya samu ACM Kalu da laifukan da suka hada da kisan kai, da fasa gida, da […]