Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

An fara kwaso yaran da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, bayan sun tsere zuwa Jamhuriyar Kamaru, da nufin hada su da iyayensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

Wasu daga cikin yaran dai marayu ne yayin da wasu kuma har yanzu iyayensu na nan da rai kuma an kwaso su ne cikin jirgin sama, wasu daga sansanin ‘yan gudun hijira na Minaoa. Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ce ta dauki gabarar wannan aiki na sada irin wadannan yara da iyaye ko […]

Nigeria: Harin kunar bakin wake ya kashe mutane a Mubi

Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah.

Nigeria: Harin kunar bakin wake ya kashe mutane a Mubi

Akalla mutum 21 suka mutu bayan wani ya kai harin kunar bakin wake wani masallacin cikin garin Mubi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya. Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah. Dan kunar bakin […]

Ana Zaman Dar-dar a Yankin Madagali Sanadiyar Sabon Harin Boko Haram

Tun daga yammacin jiya ne mayakan Boko Haram dauke da muggan makamai suka farma kauyen Bakin Dutse cikin karamar hukumar Madagali, a jihar Adamawa kuma kawo yanzu ba’a tantance adadin mutanen da wannan sabon harin ya rutsa dasu ba.

Ana Zaman Dar-dar a Yankin Madagali Sanadiyar Sabon Harin Boko Haram

Kamar yadda wasu da suka tsallake rijiya da baya suka bayyana, mayakan na Boko Haram dauke da muggan makamai, sun soma kai farmaki ne daga yankin Bakin Dutse dake kusa da garin Gulak hedikwatar karamar hukumar suna harbe-harbe ba kakkautawa inda aka dauki dogon lokaci ana dauki ba dadi a tsakaninsu da sojoji da kuma […]

Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Editan BBC na Abuja, Naziru Mikailu ya yi kicibis da wani mutumin garin Bama dake jihar Borno, wanda yanzu yake Abuja, kuma wanda mayakan Boko Haram suka sace matarsa da ‘ya’yansa biyar, a cikin shekaru 4 da suka gabata. Ya dai nemi sakaya sunansa saboda matsalar tsaro. Ya fara da bayyana makasudin dalilin barin gidansa […]

‘Yan gudun hijra na karo-karo don ba ‘ya’yansu ilimi

‘Yan gudun hijra na karo-karo don ba ‘ya’yansu ilimi

Halin tagayyara da dugunzumar da rikicin ‘yan ta-da-kayar-baya na Boko Haram ya jefa wasu ‘yan gudun hijira, ba su sanyaya musu gwiwar ilmantar da ‘ya’yansu ba a sansanonin da suke samun mafaka. ‘Yan gudun hijirar sun tashi tsaye don nema wa ‘ya’yansu mafita ta hanyar kafa makarantar Islamiyya da taimakon kungiyar Women In Da’awa. Wakiliyar […]

An Roki Nakasassu A Jihar Borno Da Su Kaurace Wa Bara.

Gwamnatin jihar Borno ta bukaci nakasassu a jihar da su jingine sana'ar bara su rungumi sana'oi, kwamishinan mata da walwalasr matasa ne MadamPanta Baba Shehu tayi wannan kiran.

An Roki Nakasassu A Jihar Borno Da Su Kaurace Wa Bara.

Gwamnatin jihar Borno tayi kira ga nakasassu a jihar da suyi wa Allah Da Ma’aikainsa su daina barace-barace akan tituna. Wannan kiran ko ya fito ne daga bakin kwamishinar harkokin mata da Walwalar matasa Malama Panta Baba Shehu, kuma tayi kiran ne sai’lin da take rarraba kayan abinci mai tarin yawa ga nakassassun. Tace gwamnati […]

Za a fara yin shari’ar ‘yan Boko Haram 1,600

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya don gurfanar da mutanen da ake tuhuma da zama mayakan kungiyar Boko Haram sama da 1,600 a gaban kotu.

Za a fara yin shari’ar ‘yan Boko Haram 1,600

Ministan Shari’a na kasar Barista Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa za a fara yi wa mutanen shari’a ne a cibiyoyi daban-daban da ake tsare da su daga watan gobe. Ma’aikatar shair’ar ta kara da cewa an bayar da shawarar sakin mutane 220 da ake zargi da zama ‘yan Boko Haram saboda babu wata […]

Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Rarraba Dubi ra’ayoyi Jiragen leken asiri na sojojin yakin saman Najeriya sun gano wasu sabbin sansanoni da kungiyar Boko Haram ke ginawa a dajin Sambisa kuma sun rugurguzasu da lugudan wuta

Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar yace jiragen leken asirinsu sun gano yunkurin wasu mayakan Boko Haram na sake kafa sabbin sansanoni a dajin Sambisa. Sun gano wurare guda hudu da yan ta’addan ke akai, dalilin ma kenan da yasa suka kaddamar da shirin sintirin OPERATION RUWAN WUTA a wannan dajin. […]

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

 A sassa daban daban na Najeriya dakarun kasar kan gudanar da atisaye na musamman inda akan jibge su su yi kwana da kwanaki ko kuma su dauki wani tsawon lokaci suna atisayen. Akan kai dakarun ne yankunan da ke fama da wasu matsaloli na musamman, misali a yankin da ake fama da matsalar satar shanu […]

‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 15 A Borno

‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 15 A Borno

‘Yan kunar bakin waken da ba asan ku su wanene ba sun kashe a kalla mutum 15 a Arewa masu Gabashin Kasar Nijeriya kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito, inda suka zanta da ma’aikatan ceto da ‘ya sintiri. An dai ce harin ya faru ne a Konduga, wajen birnin Maiduguri, babban birnin jihar […]

1 2 3 10