‘Mu rika ba marasa galihu tsofaffin littattafai’

A Najeriya, wasu matasa sun kafa wata kungiya domin tara litattafan karatu da aka fi sani da 'Text Books' da aka riga aka gama amfani da su, suna kai wa makarantun gwamnati da na marasa galihu.

‘Mu rika ba marasa galihu tsofaffin littattafai’

Kungiyar mai suna ‘Book Bank’ ta ce hakan zai taimaka matuka wajen inganta ilmi a tsakanin yara marasa galihu. An kafa kungiyar ne ta Book Bank a shekarar 2016, kuma tana gudanar da ayyukanta ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da kuma Lagos. Sa’id Saidu Malami shine shugaban kungiyar ta Book Bank da ya […]