Babu Yadda Boko Haram Zata Habaka Ba Tare da Haramtattun Kudi Ba – Osinbajo

Yayinda yake jawabi a wajen taron kwamitin dake yaki da kudaden haram a yammacin Afirka mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce babu yadda Boko Haram zata habaka daga gari daya har zuwa garuruwa da dama a Nigeria da wasu kasashen ba tare da samun haramtattun kudade ba

Babu Yadda Boko Haram Zata Habaka Ba Tare da Haramtattun Kudi Ba – Osinbajo

A wurin taro na goma sha takwas na kwamitin yaki da halasta kudaden haram a yammacin Afirka, Mataimkain Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yace matsalar halasta kudaden haram na yiwa kasashe irinsu Najeriya barazana. Farfesa Osinbajo yayi mamakin yadda wata bakar akida da ta samo asali a gari daya ta habaka har ta yadu cikin […]