An Damke Masu Safarar Mutane a Yammacin Afirka

Hukumar ‘yansandan kasa-da-kasa (INTERPOL) ta ce an damke masu safarar mutane guda 40 tare da ceto mutane 500 a wani samame a yammacin nahiyar Afirka.

An Damke Masu Safarar Mutane a Yammacin Afirka

Hukumar ‘yansandan kasa-da-kasa (INTERPOL) ta ce an damke masu safarar mutane guda 40 tare da ceto mutane 500 a wani samame a yammacin nahiyar Afirka. Hukumar ta kai wannan samame ne a lokacin da kasashen duniya ke kokawa game da cinikin bayi da aka bankado a kasar Libya. A cikin wata sanarwa da ta fitar, […]

‘Amurka Bata Yi Mana Adalci Ba’

Gwamnatin Chadi ta bayyana mamaki kan yadda Amurka ta sanya kasar cikin jerin sunayen kasashen da aka hana baki zuwa Amurka, a sabuwar dokar shugaba Donald Trump.

‘Amurka Bata Yi Mana Adalci Ba’

Madeleine Alingue, mai Magana da yawun gwamnatin Chadi, tace matakin yaci karo da kokarin Chadi na yaki da ta’addanci musamman a yankin Afirka ta Yamma da kuma duniya baki daya. Gwamnatin Chadi ta bukaci shugaba Donald Trump da ya sake nazari kan matakin wanda tace ya shafi kimar Chadi da kuma dangantakar kasashen biyu. Karkashin […]

Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai

Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Wani dan kungiyar Boko Haram da ake kira da kwamanda a tsakanin ’ya’yan kungiyar, ya yi ikirarin cewa shi ne ya jagoranci sace ’yan matan Chibok daga makaranta a shekarar 2014. ‘Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar labarai ta PRNigeria. Fiye […]

Daga Africa Za’a Rika Tantance Bakin-Haure – Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da wasu shugabanin kasashen turai, yayin tattaunawa da shugabannin kasashen Nijar da Chadi, Muhammadou Issoufou da kuma Idris Deby kan yadda za'a shawo kan matsalar kwarar bakin haure zuwa turai.

Daga Africa Za’a Rika Tantance Bakin-Haure – Macron

A lokacin zaman taron da aka gudanar a jiya Litinin a birnin Paris kan matsalar bakin haure, tsakanin wasu kasashen nahiyar Afrika da na Turai, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bada shawarar cewa, daga sansanonnin tattara bakin hauren dake cikin kasashen Niger da Chadi za’a rika tantance ‘yan kasashen da suka cancanci zama ‘yan gudun […]

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun halaka mutane 15 suka kuma yi garkuwa da wasu mutane takwasa a wani kauye da ke kusa da iyakar Najeriya a yankin garin Kolofota na kasar Kamaru.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun harbe mutane 15 har lahira, kana suka yi garkuwa da wasu takwas a wani kauye da ke arewacin kasar Kamaru.Jami’ai sun ce ‘yan bidigar sun yi ta bude wuta ne akan kauyen Gakara da bindgogi masu sarrafa kansu, da tsakar daren Alhamis har zuwa […]

Nigeria Za Ta Fara Taso Keyar Masu Laifi Su Gudu UAE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wata yarjejeniyar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda za ta fadada yaki da cin hanci da gwamnatinsa take yi da tsaron kasa da kuma bunkasa tattalin arziki.

Nigeria Za Ta Fara Taso Keyar Masu Laifi Su Gudu UAE

Yarjejeniyar ta yi tanadin musayar mutanen da suka aikata manyan laifuka tsakanin Najeriya da Hadaddiyyar Daular Larabawa. Shugaban ya bayyana al’amarin da wani muhimmin ci gaba ga kasar wanda zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da tsaro da yaki da cin hanci da ciki da wajen kasar. Sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen tasa keyar […]

Chadi Ta Rufe Ofishin Jekadancin Qatar

Kasar Chadi ta sanar da rufe ofishin Jakadancin Qatar da ke birnin Ndjamena inda ta bukaci jami’an diflomasiyar da ke aiki ciki da su fice daga kasar cikin kwanaki 10 masu zuwa.

Chadi Ta Rufe Ofishin Jekadancin Qatar

Kasar Chadi ta sanar da rufe ofishin Jakadancin Qatar da ke birnin Ndjamena inda ta bukaci jami’an diflomasiyar da ke aiki ciki da su fice daga kasar cikin kwanaki 10 masu zuwa. Wannan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Saudi Arabi da Qatar, inda Chadin tare da kasashen Mauritania da Senegal ke goyan […]

Wani Dan Boko Haram Da Ya Tuba Ya Yi Bayani

A wani al'amari mai nuna irin yadda wasu 'yan Boko Haram ke waswasin dorewar kungiyar da kuma halaccinta, wani dogarin tsaron wani na hannun daman Abubakar Shekau ya yi watsi da kungiyar tare kuma da yin wasu bayanai.

Wani Dan Boko Haram Da Ya Tuba Ya Yi Bayani

WASHINGTON D.C. —  A cigaba da gane gaskiya da wasu ‘yan Boko Haram ke yi har su ke tuba, wani daga cikinsu da ya tuba kamar sauran, ya mika kai kuma a hirar da su ka yi da Haruna Dauda ya shaida masa cewa: “Suna na Bara Umara shekaru na 27 kuma na fito ne […]

Kaddamar da rundunar sojin Sahel sai da taimakon kasashen Duniya

Kasar Mali ta bukaci taimakon kasashen duniya wajen samun kudade da makamai domin kaddamar da rundunar sojin Sahel wadda za ta yi yaki da yan ta’adda dake ci gaba da kai munanan hare hare a Yankin.

Kaddamar da rundunar sojin Sahel sai da taimakon kasashen Duniya

Jakadan Mali a Majalisar Dinkin Duniya Issa Konfourou, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewar harin da aka kai Burkina Faso da ya hallaka mutane 18 da wanda aka kai Mali da ya kashe mutane 9 ya dada tababtar da muhimancin kaddamar da rundunar sojoji 5,000 da kasashen Nijar da Mali da Chadi da Mauritania da kuma […]

‘Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Mayakan Boko Haram fiye da 240 ne suka mika wuya, bayan farmaki ta sama da kasa da dakarun hadin guiwa na kasa da kasa (MNJTF) suka kai a maboyarsu.

‘Yan Boko Haram 240 sun mika wuya bayan farmakin soji

Wata sanarwa da rundunar ta MNJTF ta fitar, ta bayyana cewa yawancin mayakan sun fito ne daga yankin na tafkin Chadi. Ta kara da cewa mayakan sun mika wuyan ne a sashe na biyu na sansanin soja a yankin Bagasola da ke kasar Chadi. Dakarun na MNJTF da suka fito daga Najeriya, Chadi, Nijar da […]