Mummunar Guguwa Ta Juye Ambaliyar Ruwa a Texas

Sama da mutum dubu guda aka tseratar daga yankunansu bayan mahaukaciyar guguwar nan da ta afkawa jihar Texax a Amurka ta haifar da kakkarfan ruwan saman daya juye zuwa ambaliyar ruwa a Houston.

Mummunar Guguwa Ta Juye Ambaliyar Ruwa a Texas

A cewar hukumar kula da yanayi ta kasar, karfi da kuma yawan ambaliyar ruwan kan ma’aunin centi mita 50 ba kakkautawa ya dakatar da zirga-zirga tare da sanya razani a zukatan mutanen yanki, lamarin daya tilasta kwashesu don kare lafiyarsu. Haka kuma yawan ruwan saman ya sanya koguna da dama yin ambaliya a yankin abin […]