Nigeria ‘Muna bayan Buhari har sai ya shekara takwas’

'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan kiraye-kirayen Shugaba Muhammadu Buhari ya koma gida ko kuma ya yi murabus saboda ya cika wata uku yana jinya a kasar Birtaniya, kamar yadda wasu 'yan kasar suka bayyana.

Nigeria ‘Muna bayan Buhari har sai ya shekara takwas’

A ranar Litinin ne wani mawaki mai suna, Charly Boy, ya shirya wata zanga-zanga a Abuja, inda aka bukaci shugaban ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka. A muhawarar da aka tafka a shafukan sada zumunta na BBC Hausa Facebook da kuma Twitter mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu. Ga kadan daga cikinsu: […]