Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Koriya Ta Arewa na ci gaba da musayar zafafan kalamai da Amurka, inda shugaba Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mai tabin hankali.

Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa da ke birnin Pyongyang ya ambato Kim Jong-un na cewa shugaban Amurka zai yaba wa aya zaki saboda jawabin da ya yi tun farkon wannan mako a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Donald Trump ya fada wa taron cewa idan tura ta kai Amurka bango, to za ta kare […]

Biranen da Zasu Kare Yarjejeniyar Muhalli a Duniya

Kasar Denmark ta kadadmar da wani kawancen biranen duniya da za su taimaka wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar kare muhallin da aka kulla a Paris ba tare da samun matsala ba.

Biranen da Zasu Kare Yarjejeniyar Muhalli a Duniya

Shirin wanda aka kaddamar kwanaki biyu da suka wuce bayan Amurka ta tabbatar da ficewarta daga yarjejeniyar ta Paris, zai mayar da hankali ne wajen yada bayanai da fasaha tsakanin gwamnatoci da ‘yan kasuwa da kuma shugabannin al’umma. Ofishin Firaministan Denmark Lars Lokke Rasmussen ya ce, wadanda suka amince su shiga cikin wannan tafiyar da […]

China za ta haramta amfani da mota mai amfani da fetir

Kasar da aka fi cinikin motoci a duniya wato China, na shirin haramta kerawa da kuma sayar da motocin da suke amfani da man fetir da dizal.

China za ta haramta amfani da mota mai amfani da fetir

Mataimakin ministan masana’antu na kasar ya ce, tuni suka fara nazari na tsanaki, sai dai har yanzu ba su yanke shawarar lokacin da za a tabbatar da haramtawar ba. Xin Guobin ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na kasar cewa, “Wadannan matakai za su kawo sauyi wajen bunkasa kamfanonin motocinmu”. China ta kera mota miliyan […]

Hukumar Kwastan Shiyar Legas Ta Kama Tabar Wiwi da Kudinta Ya Kai N72m

Hukumar kwastan dake kula da jihohin Legas da Ogun ta kama manyan motoci cike da tabar wiwi da kudinta ya kai N72m tare da wasu kayan da suka hada da motocin alfarma.

Hukumar Kwastan Shiyar Legas Ta Kama Tabar Wiwi da Kudinta Ya Kai N72m

Hukumar kwastan mai kula da jihohin Legas da Ogun ta kama tabar wiwi mai nauyin kilogram 1590 da kudinsu suka haura N72m makonni ukun da suka gabata. Kamun na zuwa ne bayan kama buhunan shinkafa 1237 wadanda aka ce gurbatattu ne da kudinsu ya kai N15m da aka shigo dasu ta kan iyakar Najeriya da […]

Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

A baya-bayan nan ne dai shugaban na Amurka ya yabawa Kim Jun-Un kan matakin daya dauke na dakatar da shirin harba wani makami mai linzami zuwa yankin Guam na Amurka

Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

Kasar Amurka ta sanyawa wasu kamfanonin kasashen Rasha da Chana 16 takunkumi saboda abinda ta kira goyan bayan shirin nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. Takunkumin na daga cikin matakan da Amurka ke dauka na dakile samun kudade ga Koriyar domin ci gaba da gina makamin. Sakataren Baitulmalin Amurka, Steven Mnuchin ya ce abin takaici ne […]

An kama wani da hannayen mutum a jakarsa

An bayar da rahoton cewa, jami'an tsaro a gabas maso yammacin kasar China sun ga wani abun mamaki da ya razana su, a lokacin da suka kama wani da hannayen mutum zai wuce da su.

An kama wani da hannayen mutum a jakarsa

Wani bidiyo ya nuna cewar jami’ai ne suka tunkari Mista Zheng mai shekara 50 a tashar mota a Duyun, da ke lardin Guizhou, bayan da aka gano hannayen a wurin da ake yin bincike da na’urar gano abin da mutum yake dauke da shi ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata. Mai gadin wurin […]