‘Yan sandan Nigeria: ‘Evans yana nan bai mutu ba’

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa madugun da ake zargi da satar mutane Chukwuduneme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans bai mutu ba kuma jami'an tsaron kasar suna ci gaba da bincike a kansa.

‘Yan sandan Nigeria: ‘Evans yana nan bai mutu ba’

Ta bayyana hakan ne bayan wasu kafafen yada labarai a kasar sun ruwaito cewa an kashe mutumin da ake zargi da satar mutane don neman kudin fansa. Har ila yau, wasu rahotanni daga kasar cewa suka yi Evans ya tsire daga hannun jami’an tsaron kasar. Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya […]