Gwamnati Ta Dukufa Wajen Ceto Mutanen Da Aka Sace a Borno – Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin ta ceto malaman Jami'ar Maiduguri da ma'aikatan kamfanin NNPC da wani bangaren Boko Haram yake garkuwa da su.

Gwamnati Ta Dukufa Wajen Ceto Mutanen Da Aka Sace a Borno – Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ta na kokarin ganin an kubutar da mutanen da ke hannun ‘yan kungiyar Boko Haram da aka kamasu a lokacin da suke binciken albarkatun man fetur a jihar Borno. Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da wani kamfanin sarrafa shinkafa a birnin Arugungu […]