Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya saka hannu kan wata sabuwar doka da za ta ba kananan masana'antu da 'yan kasuwa damar su bayar da dabbobi da wasu kayan amfani a gida a zaman jingina wajen samun bashi.

Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Hukumomin kasar dai sun ce an kafa dokar ne domin shawo matsalar rashin jari da kananan masana’antu ke fuskanta sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Wannan dokar ta bai wa bankuna kasuwanci a Zimbabwe damar su karbi dabbobi kamar shanu, da awaki, da kuma tumaki a zaman jingina wajen bayar da rancen kudi. […]