‘Malamai 70 sun bar jami’ar Maiduguri saboda Boko Haram’

Kungiyar malaman jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a Najeriya, ta ce daga 2009 kawo yanzu malaman jami'ar guda 70 ne suka bar jami'ar sanadiyar ricikin Boko Haram.

‘Malamai 70 sun bar jami’ar Maiduguri saboda Boko Haram’

Mai magana da yawun kungiyar, Dr. Danny Mamman ya ce rashin tabbas da rikicin na Boko Haram ya haifar ne ya janyo malaman suka bar jami’ar. Sai dai kuma ya ce duk da rikicin na Boko Haram har yanzu akwai mutanen da ke neman aiki a jami’ar sannan kuma dalibai ba na zuwa karatu jami’ar. […]