Sarakuna A Taraba Sun Yi Kiran A Samu Zaman Lafiya A Yankin Gembu

Biyo bayan irin yawan kashe kashen da suka auku a yankin Gembun jihar Taraba musamman tsakanin manoma da makiyaya sarakunan yankin sun gargadi al'ummominsu da su rungumi zaman lafiya, suyi watsi da makamansu su kuma kiyaye yin kalamun da ka harzuka mutane

Sarakuna A Taraba Sun Yi Kiran A Samu Zaman Lafiya A Yankin Gembu

WASHINGTON DC — Shugabannin gargajiya na yankin Gembu dake jihar Taraba da ya yi fama da tashe-tashen hankula da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a sun yi kira a kai zuciya nesa don samun dawamammiyar zaman lafiya. Sarkin Mambila Dokta Shehu Audu Baju na biyu ya furta haka lokacin da yake jawabi a fadarsa […]