Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Komawa gida da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Asabar bayan kwashe sama da wata uku yana jinya a Landan za ta taso da batutuwa daban-daban.

Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Shugaban, wanda ya fice daga kasar ranar takwas ga watan Mayu domin yin jinyar cutar da ba a bayyana ba, ya mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo. Tun daga lokacin da ya bar kasar, mukaddashin shugaban kasar ya gudanar da ayyuka da dama da suka hada da rantsar da sabbin ministoci da bai wa […]

Kotu ta mallakawa gwamnati kadarorin Diezani

Wata babbar kotun da ke Lagos ta mallaka wa gwamnatin Najeriya kaddarorin tsohuwar ministar man Najeriya, Diezani Alison-Madueke, da suka kai $40, wato kimanin naira biliyan 14.

Kotu ta mallakawa gwamnati kadarorin Diezani

Kotun ta mallaka wa Najeriya wani katafaren gidan Ms Diezani da ke yankin Banana Island da ke Lagos, wanda kudinsa ya kai $37.5m, kimanin naira biliyan 13. Haka zalika, mai shari’a Chuba Obiozor ya mallaka wa gwamnatin Najeriya naira sama da naira miliyan 84 da kuma sama da dala miliyan biyu, wasu kudaden da aka […]