Trump na fuskantar bore kan rikicin Charlottesville

Shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar bore tun bayan furta wasu kalamai kan rikicin kabilancin daya faru a Charlottesville, al’amarin da yanzu haka ke ci gaba da sanyaya guiwar magoya bayansa, har ta kai ga murabus din wani babban jigo a tafiyar shugaban.

Trump na fuskantar bore kan rikicin Charlottesville

Lamarin dai ya buda sabon babi a tafiyar mulkin Shugaba Trump tun bayan fara aikinsa sama da kwanaki dari biyu. Kalaman na Trump dai na zargin bangarorin 2 da alhakin tayar da tarzomar wadda ta girgiza dan karamin garin na Charlottesville da ke Jihar Virginia, tare da sanadin mutuwar wata mace guda cikin masu zanga-zangar […]