Buhari ya Kammala Tsara Kasafin Kudin 2018

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2018 a wajen taron mako-mako na majalisar da aka yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasa a Abuja.

Buhari ya Kammala Tsara Kasafin Kudin 2018

Majalisar zartarwar ta ce nan ba da jimawa ba ne za a gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokoki ta kasar. Ministan Ayyuka, Wutar Lantarki da Gidaje Babatunde Fashola, ya ce aikin shugaban kasar ne ya mika wa majalisar kasafin kudi kuma ya yi bayanin kan yadda za a kashe kudin. Har ila yau ministan […]

Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

A kalla mutum 62 sun mutu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan wata cutar da ba a san hakikaninta ba ta barke.

Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar jihar ta fitar ta ce wadanda suka kamu da cutar suna cin ciwon mara baya ga amai da gudawa da suke yi. Sanarwar ta ce daga farko dai an kai wadanda suka kamu da cutar asibitin koyarwar gwamnatin tarayyar kasar da ke jihar Edo, inda aka gane cewar ba zazzabin […]

An cafke mutane 24 da ake zargi ‘Yan Boko Haram ne a Jihar Edo

An cafke mutane 24 da ake zargi ‘Yan Boko Haram ne a Jihar Edo

Rundunar Sojan Najeriya ta bada sanarwar cafke wasu mutane ashirin da hudu wadanda ake zargin ‘yan kungiyar tada kayar baya ne, ta Boko Haram. Babban kwamandan Makarantar Horar da aikin Injiniya ta Sojan Najeriya dake garin Auchi a Jihar Edo ne ya sanar da hakan lokacin da ya ziyarci fadar basaraken Gargajiya na Masarautar Auchi, […]