Buhari bai iya mulki ba — Shekarau

Buhari bai iya mulki ba — Shekarau

Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bata tabuka wani abun azo a gani ba a tsawon fiye da shekara uku da ta yi kan mulkin kasar. Malam Ibrahim Shekarau, wanda ke neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya shaida […]

Badaƙalar Biliyan 2.1: Maina Ya Ƙalubalanci EFCC …Ya Ce Yana Bin Gwamnati Bashin Biliyan 159

Maina ya yi wannan ƙalubale ne ta hannun lauyansa, Barista Sani Katu, inda ya ce bai saci ko ficika ba, sai dai ma tulin bashin da yake bin gwamnatin tarayya na Naira Biliyan 159.

Badaƙalar Biliyan 2.1: Maina Ya Ƙalubalanci EFCC …Ya Ce Yana Bin Gwamnati Bashin Biliyan 159

Tsohon Jagoran Fansho, Abdulrasheed Maina ya ƙalubalanci Hukumar EFCC da ta zo a baje zarginsa da ta ke yi kan badaƙalar Naira Biliyan 2.1 a faife. Inda tsohon jagoran fanshon ya ce, a tsarkake yake kuma baya tsoron a yita ta ƙare. Maina ya yi wannan ƙalubale ne ta hannun lauyansa, Barista Sani Katu, inda […]

EFCC Bata Bincike Na – Sheikh Pantami

Shugaban Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA), Sheikh Isa Pantami, ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake cewa Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa tana bincikensa.

EFCC Bata Bincike Na – Sheikh Pantami

Wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ruwaito Ministan Sadarwar kasar Adebayo Shittu yana cewa gwamnatin tarayya tana jiran sakamakon wani binciken da hukumar EFCC take wa shugabannin hukumar NITDA. Rahotannin sun ce ana binciken hukumar ne kan yadda ta kashe kudin da aka ware mata a kasafin kudin shekarar 2017, bayan wani korafi […]

Ina Hakkokin Masu Taimaka Wa EFCC Da Bayanai

Ina Hakkokin Masu Taimaka Wa EFCC Da Bayanai

A Najeriya, sama da watanni shida bayan da wasu suka tseguntawa hukumar EFCC da bayanai don gano bilyoyin kudaden da aka boye a wani gida da ke unguwar Ikoyi a birnin Lagos, har yanzu gwamnati ba ta bai wa wadanda suka taimaka da bayanai domin gano kudaden hakkokinsu na 5% da doka ta ce a […]

EFCC Ta Tabbatar Da Shirin Taso Keyar Madueke Zuwa Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, EFCC ta tabbatar da shirin taso keyar tsohuwar Ministan mai, Diezani Aison Madueke daga Ingila zuwa Najeriya.

EFCC Ta Tabbatar Da Shirin Taso Keyar Madueke Zuwa Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan Najeriya sun bukaci hukumomi da su taso keyar tsohuwar Ministar saboda zargin ta da cin hanci da rashawa. Tuni dai, kotu da mallaka wa gwamnatin Najeriya wasu kadarori na biliyoyin Naira da aka kwato daga hannun Madueke bayan ta tara su ta haramtacciyar hanya. Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu […]

Masu Gangamin “Mumu don Do” Na Neman A Dawo da Tsohuwar Ministan Man Fetur daga Ingila

Biyo bayan irin makudan kudin da aka ce an gano tsohuwar ministar man fetur Alison Madueke ta wawure daga kamfanin NNPC masu gangamin "mumu don do" sun bukaci hukumar EFCC ta dawo da ita daga Ingila

Masu Gangamin “Mumu don Do” Na Neman A Dawo da Tsohuwar Ministan Man Fetur daga Ingila

Mabiya gangamin na Charlie Boy da ake yiwa lakabin “Our Mumu Don Do” sun gudanar da wata zanga zanga a Abuja yau saboda neman hukumar EFCC ta dauki matakan dawo da tsohuwar ministar man fetur daga Ingila inda nan ma an zargeta da wawurare kudade mallakar gwamnatin Najeriya. Kasa da makonni biyu ke nan da […]

Kotu Ta Amince Gwamnati Ta Rike Kudaden Diezani

Biyo bayan karar da hukumar EFCC ta shigar yanzu wata kotun Legas ta tabbatarwa gwamnatin tarayyar Najeriya mallakar kudaden da aka gano tsohuwar ministar man fetur Alison Madueke ta wawure

Kotu Ta Amince Gwamnati Ta Rike Kudaden Diezani

Ranar 9 ga wannan watan ne Justice Chuka Obiozo na kotun tarayya dake Legas ya zartas da hukumci na wucin gadi da ya mallakawa gwamnatin tarayya makudan kudaden da aka gano su cikin bankin Stirlin. Hukumcin alkalin ya biyo karar da hukumar EFCC ta shigar ne. A hukumcin farko alkalin ya umurci bakin ko kuma […]

Mene ne Shugaba Buhari Bai Fada Ba a Jawabinsa?

Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar Najeriya jawabi, akwai wasu manyan batutuwa da jama'ar kasar suke ganin ya dace shugaban ya tabo amma bai yi maganarsu ba.

Mene ne Shugaba Buhari Bai Fada Ba a Jawabinsa?

Akwai masu ganin cewa jawabin shugaban ya fi mayar da hankali ne a kan mayar da martani ga masu fafutikar ballewa daga Najeriya. Sai dai jawabin ya tabo batun tsaro musamman yaki da Boko Haram da satar mutane don neman kudin fansa da kuma rikicin Fulani makiyaya da manoma. Har ila yau akwai al’amura da […]

Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Komawa gida da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Asabar bayan kwashe sama da wata uku yana jinya a Landan za ta taso da batutuwa daban-daban.

Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Shugaban, wanda ya fice daga kasar ranar takwas ga watan Mayu domin yin jinyar cutar da ba a bayyana ba, ya mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo. Tun daga lokacin da ya bar kasar, mukaddashin shugaban kasar ya gudanar da ayyuka da dama da suka hada da rantsar da sabbin ministoci da bai wa […]

1 2 3