Komitin Sulhu na MDD Zai Dauki Mataki Kan Korea ta Arewa Littini

Littinin nan ne Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke zama na musamman domin tattauna batun sake gwajin makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi, don duba irin matakin da ya dace a dauka.

Komitin Sulhu na MDD Zai Dauki Mataki Kan Korea ta Arewa Littini

Kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Japan da Korea ta Kudu suka bukaci zaman na musamman  na littini. Tun jiya lahadi Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da ayarin mashawartansa game da harkokin tsaro inda suka duba gwaji na baya-bayan nan na makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi. Sakataren Watsa labarai na Ofisshin Shugaban […]

Faransa Za Ta Yi Amfani Da Jirage Masu Makamai Da Ke Sarrafa Kan Su

Yanzu haka dai kasar za ta fara amfani da jiragen masu makamai da ke sarrafa kan su, sabanin wanda tun da farko ta ke amfani da su wajen tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan sintiri.

Faransa Za Ta Yi Amfani Da Jirage Masu Makamai Da Ke Sarrafa Kan Su

Ministar tsaron Faransa Florence Parly, ta ce kasar za ta fara yin amfani da jirage masu sarrafa kan su wadanda ke dauke da makamai a maimakon wadanda ke gudanar da ayyukan sintiri da kuma tattara bayanan sirri kadai. Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke gabatar da jawabi a gaban taron shekara […]

‘Cigaban Afirka ne Kawai Zai Magance Matsalar Bakin-Haure’

Shugabanin kasashen Nijar da Chadi sun bayyana cewa, cigaban kasashen Afirka ne kawai, zai magance yadda matasa ke barin kasashen nahiyar suna tafiya Turai suka da tarin hadurran da ke tattare da hanyoyin da suke bi.

‘Cigaban Afirka ne Kawai Zai Magance Matsalar Bakin-Haure’

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou yayin gaisawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a fadar gwamnati da ke birnin Paris, 28 ga watan Agusta, 2017. Shugabanin kasashen Nijar da Chadi sun bayyana cewa, cigaban kasashen Afirka ne kawai, zai magance yadda matasa ke barin kasashen nahiyar suna tafiya Turai suka da tarin hadurran da ke tattare […]

Daga Africa Za’a Rika Tantance Bakin-Haure – Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, tare da wasu shugabanin kasashen turai, yayin tattaunawa da shugabannin kasashen Nijar da Chadi, Muhammadou Issoufou da kuma Idris Deby kan yadda za'a shawo kan matsalar kwarar bakin haure zuwa turai.

Daga Africa Za’a Rika Tantance Bakin-Haure – Macron

A lokacin zaman taron da aka gudanar a jiya Litinin a birnin Paris kan matsalar bakin haure, tsakanin wasu kasashen nahiyar Afrika da na Turai, Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bada shawarar cewa, daga sansanonnin tattara bakin hauren dake cikin kasashen Niger da Chadi za’a rika tantance ‘yan kasashen da suka cancanci zama ‘yan gudun […]