“Dole gwamnatin Najeriya ta kare ‘yan gudun hijira”

Hukumar jin-kai ta duniya ta bayyana cewa, dole ne gwamnatin Najeriya ta inganta matakan tsaro don kare lafiyar mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

“Dole gwamnatin Najeriya ta kare ‘yan gudun hijira”

Wannan na zuwa ne bayan mutane 28 sun rasa rayukansu sakamakon wani kazamin hari da ake zargin Boko Haram da kai wa a sansanin ‘yan gudun hijirar a yammacin jiya Talata. Hukumar ta ce, sansanin ‘yan gudun hijira, wani tudun mun-tsira ne ga mutanen da suka guje wa tashin hankali , amma kuma saboda sakaci, […]