Ana ruguguwar ficewa Florida kafin isowar guguwar Irma

Dubban mutane ne ke ruguguwar ficewa Florida a Amurka kafin isowar mahaukaciyar guguwar Irma da yanzu haka ta isa Cuba dauke da iska mai karfi da ruwan sama.

Ana ruguguwar ficewa Florida kafin isowar guguwar Irma

Guguwar Irma ta isa Cuba bayan ta yi barna a wasu tsibaran yankin Caribbean. Guguwar da aka ce yanzu ta kai rukuni na biyar na gudu ne a kilomita 190. Guguwar ta tsallake Bahamas ta fada Cuba. Amurka ta bukaci mutane Miliyan 6 su kaurace a yayin da guguwar ta doshi Florida. Akalla mutane 20 […]