Shi’a Ta Ki Tattaunawa Da Kwamitin Gwamnati a Najeriya

Kungiyar mabiya shi’a da ke Najeriya ta sanar da shirin kauracewa zaman tattaunawar kwamitin bincike da gwamnatin tarayyar ta kafa kan kisan mabiyanta sama da 300 da ake zargin sojin kasar da aikatawa.

Shi’a Ta Ki Tattaunawa Da Kwamitin Gwamnati a Najeriya

Kungiyar ta ce la’akari da irin mutanen da aka zaba a kwamitin da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kafa na mutum 7, ba a shirya mata adalci ba. Dambarwa dai ta faro ne tsakanin bangaren gwamnatin da kuma kungiyar ta Shi’a tun bayan wata hatsaniya data faru a karshen shekarar 2015 tsakanin dakarun […]