Mutane 40 Sun Mutu a Zabtarewar Kasa a Congo

A kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu sakamakon zabtarewar kasa da ta lullube wani dan karamin kauyen masunta a Jamhuriyar Demokradiyar Congo a gabar kogin Albert da ke yankin Ituri a arewa maso gabashin kasar.

Mutane 40 Sun Mutu a Zabtarewar Kasa a Congo

Pacifique Keta mataimakin gwamnan yankin Ituri ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labara na AFP cewa lamarin ya faru ne a kauyen Tora, in da mutane 40 suka rasa rayukansu. Shugaban asibitin Tshomia da ke Tora a yankin Ituri,  Hervé Isamba ya ce, mutane 4 sun tsira da rayukansu daga cikin wadanda aka kwantar su a […]

Saliyo: Za a Yi Wa Daruruwan Gawawwaki Jana’izar Gama-gari

Yau Alhamis ne gwamnatin kasar Saliyo ta ce za a yi wa wadanda aka tabbatar sun mutu sakamakon ambaliya da zaftarewar kasa a wajen babban birnin kasar, jana'izar gama-gari.

Saliyo: Za a Yi Wa Daruruwan Gawawwaki Jana’izar Gama-gari

Amma wasu jami’an kiwon lafiya a Saliyon sun ce an binne kusan rabin mutane 400 da kawo yanzu aka san sun mutu sakamakon ibtila’in na ranar Litinin a birnin na Freetown, gabanin jana’izar ta hukuma saboda sun fara rubewa. ”Tun jiya sun gano fiye da gawawwaki 400 kuma an binne kusan 150 cikin dare, wadanda […]

Siera Leone: Zabtarewar laka ta kashe mutum 300

Akalla mutane 300 ne suka mutu a Freetown, babban birnin Saliyo, bayan da laka ta binne su a cikin gidajensu da ke wani yankin birnin.

Siera Leone: Zabtarewar laka ta kashe mutum 300

Lamarin ya auku ne a yankin Regent da sanyin safiyar Litinin bayan ruwan sama mai kama da bakin kwarya, kuma lakar ta binne gidaje da yawa. Wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ce da alama mutane da dama na barci a lokacin da zabtarewar lakar ya faru. Kawo yanzu ba a san yawan wadanda […]

Mutane 312 sun mutu a ambaliyar Saliyo

Akalla mutane 312 ne suka rasa rayukansu, in da sama da dubu 2 suka rasa gidajensu sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa a babban birnin Freetown na Saliyo a yau Litinin.

Mutane 312 sun mutu a ambaliyar Saliyo

Rahotanni na cewa, dakunan ajiye gawarwaki sun cika makil, kuma jama’a na ci gaba da neman ‘yan uwansu da makusantansu. Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ce, ya shaida yadda aka yi ta kwashe gawarwakin mutane da kuma yadda gidaje suka nutse a ruwa musamman a wasu yankuna biyu na birnin, in da […]