Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa kimanin rayuka hudu ne aka rasa a wani sabon rikici dake neman barkewa a tsakanin Fulani Makiyaya da kabilun yankin Kwateh a yankin karamar hukumar Girei.

Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

An tabbatar da cewa rikicin na neman tashi ne biyo bayan kashe wasu Fulani makiyaya biyu, inda suma fulanin suka kashe wasu mutanen yankin biyu a wani harin daukar fansa. To sai dai tuni wannan lamarin yakai ga fara kona gidajen wasu Fulani makiyaya a yankin, kamar yadda shugaban karamar hukumar Girein Alhaji Hussaini Masta, […]

Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

A kalla mutum 62 sun mutu a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, bayan wata cutar da ba a san hakikaninta ba ta barke.

Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar jihar ta fitar ta ce wadanda suka kamu da cutar suna cin ciwon mara baya ga amai da gudawa da suke yi. Sanarwar ta ce daga farko dai an kai wadanda suka kamu da cutar asibitin koyarwar gwamnatin tarayyar kasar da ke jihar Edo, inda aka gane cewar ba zazzabin […]

“An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba”

“An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba”

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar a matsayin kisan-kare-dangi. Babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ya bayyana hakan, ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila. Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a […]