Burin Kwankwaso Na Tsayawa Takarar Shugaban Kasa Na Daga Cikin Abin Da Ya Haifar Da Baraka A Kano – Sanata Barau

Burin Kwankwaso Na Tsayawa Takarar Shugaban Kasa Na Daga Cikin Abin Da Ya Haifar Da Baraka A Kano – Sanata Barau

Shugaban Kwamitin Manyan Makarantu da Asusun Talafawa Manyan Makarantu TETFUND, Sanata Barau Jibrin (APC Kano) a wata hira da yayi ya bayyana wasu dalilai guda biyu wadanda suka saka za a cigaba da samun rashin fahimta tsakanin Kwankwaso da Ganduje Menene Yasa Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje Yaki Ci Yaki Cinyewa? Abubuwa ne guda biyu […]

Bamusan Inda Ganduje Ya Dosa Ba – Danburam Nuhu Yakasai

Bamusan Inda Ganduje Ya Dosa Ba – Danburam Nuhu Yakasai

Zaka Iya Fada Mana Menene Yasa Magoya Bayan Kwankwaso Da Ganduje Fada? Kwankwasiyya Kungiya ce mai girmama doka da oda. Bamu fito don muyi fada ba, bamu fito don kai farmaki kan kowa ba. Abun da ya faru shi ne, mu magoya bayan Kwankwasiyya mun fito yadda muka saba gudanar da bukukuwan sallah da kuma […]

Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Hada Wata Tawaga Ta Kwararru Don Suyi Bincike Kan Fadan Da Ya Faru Ranar Hawan Daushe

Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Hada Wata Tawaga Ta Kwararru Don Suyi Bincike Kan Fadan Da Ya Faru Ranar Hawan Daushe

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Mr Rabi’u Yusuf, ya kaddamar da wata tawaga ta kwararrun ‘yan sanda don suyi bincike kan fadan da aka gwabza ranar Asabar tsakanin dariku biyu na Jam’iyyar APC a cikin birnin Kano. Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Magaji Majiya ne ya sanar da hakan yayin da yake ganawa da […]

Fadan Ranar Hawan Daushe: ‘Yan Kwankwasiyya sun sake shigar da korafi zuwa Hukumar ‘Yan Sanda

Fadan Ranar Hawan Daushe: ‘Yan Kwankwasiyya sun sake shigar da korafi zuwa Hukumar ‘Yan Sanda

Wata tawagar ‘Yan Jam’iyar APC tsagin Kwankwasiyya daga Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Rabiu Suleiman Bichi sun sake shigar da sabon korafi jiya zuwa Hukumar ‘Yan Sanda kan rikicin kwananan da ya faru tsakaninsu da magoyan bayan Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje Da yake Magana a madadin tawagar bayan shigar da korafin, tsohon Kwamishinan jihar […]

Fadan Ranar Hawan Daushe: An Gargadi Matasa Kan Rigingimun Siyasa

Fadan Ranar Hawan Daushe: An Gargadi Matasa Kan Rigingimun Siyasa

Kungiyar Matasan Nijeriya (YAN) Sashin Jihar Kano sun gargadi matasa da kada su bari wasu ‘yan siyasa su ringa amfani dasu don haifar da tashin hankali a jihar. Kiran na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Kungiyar, Komred Bashir Bello Roba ya sanyawa hannu. Sanarwa ta ce kiran ya zama dole ne duba da […]

Kwankwasiyya Tayi Barazanar Zuwa Kotu Sakamakon Fadan Da Ya Faru A Kano Da Gandujiyya

Kwankwasiyya Tayi Barazanar Zuwa Kotu Sakamakon Fadan Da Ya Faru A Kano Da Gandujiyya

A kalla mutane 20 ‘Yan Darikar Kwankwasiyya aka tabbatar an jiwa rauni bayan barkewar fada tsakanin masoyan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da masoyan wanda ya gada a mulki Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso. Magoya bayan ‘yan siyasar biyu sun gwabza fada a harabar fadar mai martaba yayin Hauwan Dushe ranar  Asabar. Yayin da yake tabbatar da […]

Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Gwabza Fada Tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya Da ‘Yan Gandujiyya A Kano

Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Gwabza Fada Tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya Da ‘Yan Gandujiyya A Kano

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Rabi’u Suleiman Bichi da kanin tsohon gwamnan jihar Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso na daga cikin mutane da daman da suka ji rauni jiya sakamakon gwabza fada tsakanin magoya bayan darikar Kwankwasiyya da Gandujiyya. Sauran wadanda aka jiwa rauni a fadar mai martaba lokacin da ake gudanar da Hawan Dushen […]

Kwankwaso ko Ganduje: Waye sahihin jagoran APC a Kano?

Wata wasika da shugaban jami'iyyar APC na Arewa maso Yamma ya aika, wacce ke goyon bayan Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar Kano, na tayar da jijiyoyin wuya tsakanin magoya bayan Gandujiyya da Kwankwasiyya.

Kwankwaso ko Ganduje: Waye sahihin jagoran APC a Kano?

Tuni dai tsagin kwankwasiyya ya yi watsi da takardar, wacce ta nemi Abdullahi Abbas na tsagin Gandujiyya ya ci gaba da rike shugabancin jam’iyyar a Kano. Umar Haruna Doguwa na tsagin kwankwasiyya ya dage kan cewa har yanzu shi ne shugaban APC a Kano, don kuwa takardar ba umarnin uwar jam’iyyar ba ne. Kimanin wata […]