Biranen da Zasu Kare Yarjejeniyar Muhalli a Duniya

Kasar Denmark ta kadadmar da wani kawancen biranen duniya da za su taimaka wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar kare muhallin da aka kulla a Paris ba tare da samun matsala ba.

Biranen da Zasu Kare Yarjejeniyar Muhalli a Duniya

Shirin wanda aka kaddamar kwanaki biyu da suka wuce bayan Amurka ta tabbatar da ficewarta daga yarjejeniyar ta Paris, zai mayar da hankali ne wajen yada bayanai da fasaha tsakanin gwamnatoci da ‘yan kasuwa da kuma shugabannin al’umma. Ofishin Firaministan Denmark Lars Lokke Rasmussen ya ce, wadanda suka amince su shiga cikin wannan tafiyar da […]