Mutane 40 Sun Mutu a Zabtarewar Kasa a Congo

A kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu sakamakon zabtarewar kasa da ta lullube wani dan karamin kauyen masunta a Jamhuriyar Demokradiyar Congo a gabar kogin Albert da ke yankin Ituri a arewa maso gabashin kasar.

Mutane 40 Sun Mutu a Zabtarewar Kasa a Congo

Pacifique Keta mataimakin gwamnan yankin Ituri ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labara na AFP cewa lamarin ya faru ne a kauyen Tora, in da mutane 40 suka rasa rayukansu. Shugaban asibitin Tshomia da ke Tora a yankin Ituri,  Hervé Isamba ya ce, mutane 4 sun tsira da rayukansu daga cikin wadanda aka kwantar su a […]