An Zargi ‘Yan Rohingya Da Kashe ‘Yan Hindu

Rundunar sojan Bama ta zargi Musulmi 'yan ta-da-kayar-baya na Rohingya da kashe mace 20 da namiji takwas har ma da yara, wadanda ta ce ta gano gawawwakinsu a wani makeken kabari.

An Zargi ‘Yan Rohingya Da Kashe ‘Yan Hindu

Sojojin sun ce gawawwakin da suka gano na ‘yan Hindu ne, wadanda dubbansu ke cewa ‘yan ta-da-kayar-bayan sun tilasta musu tserewa daga kauyukansu. Ba a dai iya tantance sahihancin wannan bayani na rundunar sojan Myanmar ba. Musulmai ‘yan Rohingya dubu 430 ne suka gudu daga Myanmar zuwa Bangladesh, sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa […]