Ambaliya: Trump na neman dala biliyan 8

Shugaban Amurka Donald Trump na neman dala biliyan 8 domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

Ambaliya: Trump na neman dala biliyan 8

Shugaba Donald Trump na Amurka ya nemi majalisar dokokin kasar ta ba shi kusan dala biliyan 8 a matsayin tallafin da za a taimaka wa wadanda bala’in ambaliya ya shafa a Texas. A wasikar da ke kunshe da wannan bukata wadda aka gabatar ga kakaki majalisar wakilan Amurka, Paul Ryan, darektan kasafin kudi na fadar […]

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas

A karo na biyu cikin mako guda, shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa, Melania Trump za su sake kai ziyara jihar Texas domin jajintawa mutane da kuma ganewa idununsu yadda guguwar Harvey ta yi barna a yankin.

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas

Yayin da yake shirin kai ziyara birnin Houston da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Texas, shugaba Donald Trump ya aika da wasika zuwa majalisar dokokin Amurka, yana neman kusan Dala biliyan 8, wadanda za a yi amfani da su domin tallafawa jihohin Texas da Louisiana. Ana sa ran, wannan bukata da shugaban ya gabatar […]

An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Hukumomin Houston a Amurka sun kafa dokar hana fitar dare domin magance matsalar satar kayan jama’a da ake samu sakamakon ambaliyar da ta mamaye birnin yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan agaji.

An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Magajin Garin Houston Sylvester Turner ya sanar da kafa dokar hana fitar daren da zata fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba. Turner ya ce suna da dubban mutanen da suka bar gidajen su domin samun mafaka a sansanonin da aka tanada, amma bata-gari na amfani da damar wajen fasa […]

Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Afkawa Birnin Houston Dake Amurka

Kamar yadda jami'ai a jihar suka nuna Houston na cikin juyayi bayan shaida wata babbar guguwa mai tafe da ruwa a cikin tarihin jihar Texas.

Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Afkawa Birnin Houston Dake Amurka

An shaida saukar ruwan sama mai yawan centimita 75, yayin da guguwar hurricane harvey ke ratsawa ta koguna – al’amarin da ya janyo ambaliyar ruwa a kan hanyoyi ya mayar da titunan birnin kamar koguna. Ana dai hasashen cewa cikin wannan makon a bana yankin zai shaida saukar ruwan sama mai yawa. An rawaito cewa […]