Lokacin Sauya Fasalin Najeriya Ya Yi – IBB

Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan batun makomar Najeriya tun bayan da takaddama tsakanin masu rajin neman kasar Biafra da kungiyar matasan arewa da suka ba kabilar Igbo wa'adin ficewa daga arewacin kasar, tsohon shugaban Najeriya a lokacin mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce lokaci ya yi da za a sauya fasalin Najeriya.

Lokacin Sauya Fasalin Najeriya Ya Yi – IBB

WASHINGTON D.C. — shugaban Najeriya a lokacin mulkin soja, Gen. Ibrahim Badamasi Babangida, ya bi sahun masu kiran da a sake wa Najeriya fasali, yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi hakan. Babangida ya yi wannan kiran ne a sakonsa da ya fitar na bikin karamar salla, wanda aka rabawa kafafen yada […]