Kawunan ‘Yan Najeriya Sun Rabu Akan Shugaba Buhari

Yayinda tun farkon makon nan wasu suke zaman dirshan har sai Shugaba Buhari ya dawo ko yayi murabus, yau ma wasu sun fito suna goyon bayan shugaban tare da kiran ya cigaba da jinyarsa har sai ya samu sauki, furucin da masana shari'a suka ce yana kan ka'aida bisa ga kundun tsarin mulkin kasa

Kawunan ‘Yan Najeriya Sun Rabu Akan Shugaba Buhari

Daga bisa alamu kawunan ‘yan Najeriya ya rabu akan Shugaba Buhari saboda suna bayyana ra’ayoyin dake cin karo da juna yayinda suke zanga zanga kullum a Abuja. Yau wani gungun matasa ya bayyana a karkashin kungiyar Good Governance and Change Initiative ko GGCI. Sun fito sun yi tasu zanga zangar ta nuna goyon bayansu wa […]