Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya dakatar da Yusuf Ogundare, wanda shi ne basaraken Shangisha a Magodo da ke cikin jihar Legas saboda kitsa shirin sace kansa da kaninsa a matsayin garkuwa.

Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

A ranar 5 ga watan Yuli ne basaraken ya bace a cikin karamar hukumar Ikosi-Isheri ta jihar Legas. A sanadiyyar wannan ne gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya dakatar da basaraken daga aiki. A wata sanarwar da kwamishinan kananan hukumomi da al’ummomi ya sanya wa hannu, ta ce gwamnan ya dakatar da basaraken daga aikinsa. […]