Sama da Ma’aikata Milyan 2 na Mutuwa Duk Shekara Sanadiyyar Aiki-ILO

Galibin ma'aikatan dai a cewar hukumar ta ILO na mutuwa ne sanadiyyar cutuka, lamarin da ke nuna cewa ma'aikatu ba su fiya mai da hankali wajen kulawa da lafiyar ma'aikatansu.

Sama da Ma’aikata Milyan 2 na Mutuwa Duk Shekara Sanadiyyar Aiki-ILO

Hukumar kwadago ta duniya ILO, ta ce akalla ma’aikata miliyan Biyu, da dubu dari hudu ne ke mutuwa a duniya duk shekara, sakamakon kamuwa da cutuka daban daban, a dalilin ayyukansu.Daraktan hukumar ta ILO Guy Ryder, ya bayyana haka ne a taron kwadago da ke gudana a Singapore karo na 21, kan inganta hanyoyin kare […]