Jirgin Kasa Ya Halaka Mutane a India

Jirgin Kasa Ya Halaka Mutane a India

Wani jirgin kasa a yankin Amritsar ya halaka mutane akalla 60 inda kuma ya raunata wasu akalla 100 a yayin da yayi kutse a cikin wasu masu taro a arewacin yankin Punjab. Su dai wadanda hatsarin ya rutsa dasu suna tsaye ne akan digar jirgin inda suke bikin Dusshera wanda aka sabayi a kasar ta […]

Indiya: Walmart ya sayi Flipkart akan $16bn

A wani mataki na kasuwanci da zuba jari da zai kasance mafi girma a kasar Indiya, kamfanin Walmart ya sanar da cewa zai sayi wani bangare da zai mallaka masa kamfanin Flipkart na Indiya.

Indiya: Walmart ya sayi Flipkart akan $16bn

Wannan cinikin zai ba Walmart damar ja da kamfanin Amazon a daya daga cikin kasuwanni mafi girma da saurin bunkasa a duniya. Bayan fiye da shekara guda ana tattaunawa, kamfanin Walmart na dab da sayen kashi 77 cikin dari na hannayen jarin kamfanin Flipkart a kan dala biliyan 16. An dai kafa kamfanin na Flipkart […]

Mutane 5 Sun Mutu Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa A Birnin Mumbai

Ruwan saman ya tsagaita a yau Laraba a Mumbai, amma kwararru a fannin yanayi sun yi gargadin cewa ta yiwu ya dawo nan da sa’o’i 48.

Mutane 5 Sun Mutu Sanadiyyar Ambaliyar Ruwa A Birnin Mumbai

A kasar India, akalla mutane 5 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa da guguwa suka haddasa a Mumbai, babban birnin kasar, a cewar jami’an gwamnati yau Laraba. Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ya sa komai ya tsaya cik a birnin jiya Talata, wanda ya hana zirga-zirga a kan tituna kuma ya sa […]

Fyade: ‘Yar shekara goma ta haihu a India

Fyade: ‘Yar shekara goma ta haihu a India

Yarinyar da akayi wa fyade a kasar Indiya wacce kotun kolin kasar ta hana a zubar wa da ciki a watan daya gabata mai shekaru goma ta haifi yarinya mace. Sai dai har yanzu yarinyar bata san ta haihu ba sakamakon tun lokacin da cikin ya bayyana aka shaida mata cewar wani dutse ne a […]

‘Yar Shekara 10 da aka yi wa Fyade a India ta Haihu

Wata yarinya 'yar shekara 10 da aka yi wa fyade a Indiya, wacce kuma kotun kolin kasar ta hana a zubar mata da cikin a watan da ya gabata, ta haifi 'ya mace.

‘Yar Shekara 10 da aka yi wa Fyade a India ta Haihu

Yarinyar dai ba ta san cewa tana shirin haihuwa ba. A lokacin da take da cikin, an shaida mata cewa akwai katon dutse a cikinta ne shi ya sa ya yi girma. An haifi jaririyar wacce ke da nauyin kilo 2.5 ne ta hanyar yi wa uwar tiyata a garin Chandigarh, da misalin karfe 3.52 […]

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 200 a India

Mummunar ambaliyar ruwan da ta afkawa wasu yankunan jihar Gujarat a kasar Indiya ta hallaka sama da mutum 218, kamar yadda jimi'an gwamnati suka tabbatar.

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutum 200 a India

Kwanaki biyu da yin ambaliyar ruwan, aka sake gano wasu karin gawawwakin sama da mutum 100. Jami’an jihar sun tabbatar da cewa, ambaliyar ruwan ta shafi a kalla mutum 450,000. A bana kadai jihohi 20 ne suka fuskanci ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasar Indiya. Haka kuma a arewa maso gabashin jihar Assam ma […]

India: Ya kashe matarsa saboda lattin kin dafa abincin dare

India: Ya kashe matarsa saboda lattin kin dafa abincin dare

‘Yan sanda a kasar India sun ce sun cafke wani dattijo mai shekara 60 da ya hallaka matarsa ta hanyar bindigewa saboda bata gama abincin dare da wuri ba. A daren Asabar ne Ashok Kumar ya dawo gida cikin maye, inda gardama ta kaure tsakaninsa da matarsa , kamar yadda wani babban jami’in ‘yan sanda […]