Samar Da Aikin Yi a Yankunan Igbo Zai Iya Kawo Zaman Lafiya – Kwararru

Bayan da babbar kotun tarayyar Najeriya ta bai wa gwamnatin kasar ikon ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta’addanci. Mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnati ta samar wa da matasan kungiyar aikin yi don samar da zaman lafiya.

Samar Da Aikin Yi a Yankunan Igbo Zai Iya Kawo Zaman Lafiya – Kwararru

An yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta tsara ingantacciyar hanyar samarwa ‘yan kungiyar IPOB aikin yi, don magance illolin dake tattare da zaman banza. Yayin da Muryar Amurka ta zanta da wasu mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, da akwai alamar cewa batun rashin aikin yi shine ya mamaye yankin ya kuma haddasa […]

Bama Bukatar Wani Sabon Yakin – Ohanaeze Ndigbo

Bama Bukatar Wani Sabon Yakin – Ohanaeze Ndigbo

Shugaban Kungiyar Igbo Zalla wato Ohanaeze Ndigbo na Kasa,  Mr. John Nwodo, yayi kira ga ‘yan Nigeriya daga kowacce kabila, addini ko nahiya da su zauna lafiya. Inda yake cewa kasar bata bukatar shiga wani yaki daban. Mr Nwodo yayi wannan maganar ne a Gombe yayin da ya jagoranci shugabannin kabilar Igbo na daukacin arewacin […]

Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation Python Dance II.

Nigeria: An tura jirgin yaki yankin Igbo

Wata sanarwar da darakatan hulda da jama’a na sojin saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya sanya wa hannu, ta ce kayayyakin aikin da sojin saman Najeriya ta tura wa jami’an aikinta na musamman a Fatakwal sun hada da jirgin yaki kirar Alpha Jet. Sanarwar ta kara da cewar an tura jirgin yankin ne domin a samar […]

Wa’adin Neman a Tsige Mahaifin Nnamdi Kanu Daga Sarauta Ya Cika

Wa'adin da wata kungiyar matasa ta bai wa gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, na ya tsige mahaifin Nnamdi Kanu, Israel Okwu Kanu daga sarautarsa, ya cika, inda suka zarge shi da kin ja wa dansa kunne kan fafutukar da yake yi wacce suka ce ta kassara harkokin yau da kullum a yankin.

Wa’adin Neman a Tsige Mahaifin Nnamdi Kanu Daga Sarauta Ya Cika

Wa’adin da wata kungiyar matasa a garin Umuahia ta bai wa gwamnatin jihar Abia na ta tsige Israel Okwu Kanu, mahaifin shugaban fafutukar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga mukamin sarautar garin Isiamah Afaraukwu ya cika. A farkon makon nan kungiyar matasan ta ba da wa’adin ga gwamna Okezie Ikpeazu inda ta yi barazanar […]

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ya yi cewar 'yan hamayya ne ke daukar nauyin kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya nuna cewar har yanzu gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda maimakon mayar da hankali kan aiki.

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na musamman kan shafukan sadarwar zamani ga Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin Facebook na tsohon shugaban kasar, cewa idan gwamnatin Najeriya ta san ‘yan hamayyar da ke daukar nauyin ‘yan IPOB, ta kama su tare da gurfanar da su gaban kotu. Mista Jonathan ya ce bai […]

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kai ‘Yan IPOB 67 Kurkuku

Wata babbar kotun Najeriya da ke kudu maso gabashin kasar ta bayar da umarnin kai a kalla mutum 67 'yan kungiyar IPOB gidan yari, kan zarginsu da hannu a tashin hankali na fafatukar kafa kasar Biafra.

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kai ‘Yan IPOB 67 Kurkuku

Sojoji sun kama yawancin mutanen da ake zargi da kasancewa ‘yan kungiyar IPOB ne kusa da Isiala Ngwa, yayin da ‘yan sanda suka kama mutum bakwai da zargin kona ofishin ‘yan sanda na Ariara da ke Aba, wata cibiyar kasuwanci a kudu maso yammacin kasar. Mutanen sun musanta zargin da ake yi musu. Sojin Najeriya […]

Sojoji Sun Fara Janyewa A Hankali Daga Aba

Sojoji Sun Fara Janyewa A Hankali Daga Aba

Rundunar Sojin Nigeriya ta fara janye jam’anta a hankali wadanda ta girke a wuraren duba ababan hawa a garin Aba bayan fadan da aka gwabza da masu zanga-zangar kafa Kasar Biyafara (IPOB) Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya wato NAN ya rawaito ranar Lahdi Gwamna Okezie Ikpeazu na fadawa manema labarai a Umuahia cewa an janye sojojin […]

IPOB: Sanatoci Zasu Gana Da Shugabannin Tsaron Kasa

IPOB: Sanatoci Zasu Gana Da Shugabannin Tsaron Kasa

Daga Abuja – Shugaban Majalisar Dattijai ta Kasa, Dr Bukola Saraki yace majalisar zata gana da Shugabannin Tsaron Kasar nan don tsara hanyar magance rikice-rikicen da suka haifar da tashin hankali a Kudu Masu Gabashin Kasar. Yace ana tsammanin ganawar nan bada dadewa ba, haka kuma ganawar zata maida hankali kan tashin hankalin da ke […]

Nijeriya Bata Bukatar Tallafi Daga Kasashen Wajen Saboda Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Wato IPOB – Gwamnatin Tarayya

Nijeriya Bata Bukatar Tallafi Daga Kasashen Wajen Saboda Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Wato IPOB – Gwamnatin Tarayya

Ministan Kasashen Wajen Nijeriya, Mr Geoffrey Onyeama, yace kasar bata bukatar wani dauki daga kasashen wajen don takaice duk wata barazana daga Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra (IPOB) A wata ganawa da manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinki Duniya dake New York ranar Jumma’a da yamma yace kasar zata iya da duk wata barazana […]

‘Yan Kabilar Igbo Mazauna Adamawa Sunyi Allah Wadai Da Ayyukan Ta’addancin Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Ta IPOB A Kudu Maso Gabashin Kasar

‘Yan Kabilar Igbo Mazauna Adamawa Sunyi Allah Wadai Da Ayyukan Ta’addancin Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Ta IPOB A Kudu Maso Gabashin Kasar

Lokacin da yake zantawa da Manema Labarai a Yola ranar Jumma’a bayan wani taro da mambobin Majalisar Tsaro ta Jihar, shugaban Cibiyar Al’adun Igbo a Jihar Adamawa Cif Obonna Paul Ibere ya zargi kungiyar ta IPOB da yunkurin kawo rikici a yankin kudu masu gabashi kasar. “Duk wanda aka samu da aikata laifin da ya […]

1 2 3