Amnesty Ta Bukaci Ayi Inciken Bacewar Mutane a Najeriya

Yayin da yau ake bikin ranar magance bacewar mutane ta duniya, kungiyar Amnesty International ta bukaci Gwamnatin Najeriya ta gaggauta binciken mutanen da suka bace ta hanyar tursasawa.

Amnesty Ta Bukaci Ayi Inciken Bacewar Mutane a Najeriya

Sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai ta nuna cewar daruruwan mutane da jami’an tsaro suka kama kan wani zargi musamman a Yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bata, kuma ‘yan uwansu sun kasa gano inda suke kuma babu wani bayani da akan makomarsu. A cikin sanarwar, Amnesty ta ambaci ikirarin da mabiya Shi’a a […]