Wa’adin Neman a Tsige Mahaifin Nnamdi Kanu Daga Sarauta Ya Cika

Wa'adin da wata kungiyar matasa ta bai wa gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, na ya tsige mahaifin Nnamdi Kanu, Israel Okwu Kanu daga sarautarsa, ya cika, inda suka zarge shi da kin ja wa dansa kunne kan fafutukar da yake yi wacce suka ce ta kassara harkokin yau da kullum a yankin.

Wa’adin Neman a Tsige Mahaifin Nnamdi Kanu Daga Sarauta Ya Cika

Wa’adin da wata kungiyar matasa a garin Umuahia ta bai wa gwamnatin jihar Abia na ta tsige Israel Okwu Kanu, mahaifin shugaban fafutukar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu daga mukamin sarautar garin Isiamah Afaraukwu ya cika. A farkon makon nan kungiyar matasan ta ba da wa’adin ga gwamna Okezie Ikpeazu inda ta yi barazanar […]