Kotun Turai ta yi watsi da bukatar Hungary da Slovakia kan ‘yan gudun hijira

'Yan gudun hijirar da galibinsu 'yan Afrika ne da 'yan gabas ta tsakiya da ke gujewa yaki a kasashensu na kwarara Nahiyar Turai ne ta Girka da Italiya.

Kotun Turai ta yi watsi da bukatar Hungary da Slovakia kan ‘yan gudun hijira

Babbar kotun Turai ta yi watsi da karar da Hungary da Slovakia suka shigar na kalubalantar tsarin karbar dubban ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka a kasashen na Turai. Hukumar Tarayyar Turai ta yaba da hukuncin Kotun, wanda yanzu ya tabbatar da tsarin raba ‘yan gudun hijirar tskanin mambobin kungiyar. Duk da dai kotun […]

An Gayyaci ‘Yan Madrid 17 Tawagar Kasashensu

Kimanin 'yan kwallon Real Madrid 17 aka gayyata tawagar kasashensu, domin zuwa wasan gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 da na 'yan kasa da shekara 21.

An Gayyaci ‘Yan Madrid 17 Tawagar Kasashensu

‘Yan wasan da za su buga wa kasashensu fafatawar shiga gasar kofin duniya sun hada da Marco Asensio da Dani Carvajal da Isco da Nacho da Sergio Ramos da Lucas Vazquez. Sauran sun hada da Cristiano Ronaldo da Luka Modric da Mateo Kovacic da Keylor Navas da Gareth Bale da Casemiro da Marcelo da Toni […]

Turai: Macron Na Jagorantar Taron Magance Kwararar Bakin Haure

A wannan Litinin Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ke jagorantar jagoranci taron kasa da kasa kan yadda za a tunkari matsalar kwararar baki zuwa Turai.

Turai: Macron Na Jagorantar Taron Magance Kwararar Bakin Haure

Taron da ke gudana a birnin Paris, zai samu halartar shugabannin wasu kasashen yankin Turai, daga ciki akwai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da takwaran aikinta na Italiya Paolo Gentiloni da kuma na Spain Mariano Rajoy, yayin da daga nahiyar Afirka Afirka za a samu halartar shugaban Nijar Issifou Mahamadou, da na Chadi Idris Deuy, […]