Ma’aikatar Shari’ar Amurka Na Binciken Mummunar Zanga-zangar Fifita Jinsin Turawa

Biyo bayan baiwa hammata iska da aka yi a taron gangamin turawa jar fata masu fifita jinsin turawa da kuma ‘yan zanga zangar da suka fito yin adawa da wannan gangamin a Jihar Virginia, an fara gudanar da bincike kan wani mai mota da ya kashe wata mata.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka Na Binciken Mummunar Zanga-zangar Fifita Jinsin Turawa

Ma’aikatar shari’a ta tarayya a nan Amurka ta fara binciken keta hakkin bil Adama dangane da wata motar da aka tuka cikin mutane har ta kashe mutum guda a wajen wata zanga zangar nuna kin jinin gangamin da Turawa ‘yan wariyar launin fata suka shirya a garin Charlottesville dake Jihar Virginia. Atoni-janar na tarayya, Jeff […]