Sanata Misau Ya Sa Zare Da ‘Yan Sandan Nigeria

Wani dan majalisar dattawa a Najeriya ya zargi rundunar 'yan sandan kasar da karbar na goro kafin ta yi wa wasu daga cikin jami'anta karin girma.

Sanata Misau Ya Sa Zare Da ‘Yan Sandan Nigeria

Sanata Mohammaed Hamma Misau wanda yake wakiltar shiyyar jihar Bauchi ta tsakiya, ya yi zargin cewa: “ana karbar kimanin naira miliyan biyu da rabi a wurin jami’an ‘yan sanda da ke bukatar karin girman.” Sai dai zargin da dan majalisar ya yi bai yi wa runduar ‘yan sandan kasar dadi ba, domin kuwa sau biyu […]