An killace mutum 60 a Kano saboda kyandar biri

Hukumomin lafiya a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun ce an killace mutum 60 bayan da suka yi mu'amala da wani mara lafiya da ake zargin ya kamu da cutar kyandar biri.

An killace mutum 60 a Kano saboda kyandar biri

A karshen makon nan ne kwamishinan lafiya na jihar, Dr Kabir Getso, ya ce: “an gano alamun cutar ne a tare da mara lafiyar, sai dai muna zargin cewa tasa cutar ta fi kama da farankama maimakon kyandar biri.” A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya yi watsi da zargin da ake […]