‘Yan majalisar dokokin Kano 6 sun sauya sheka

‘Yan majalisar dokokin Kano 6 sun sauya sheka

Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kano mutum shida sun sauya sheka daga Jam’iyyar APC izuwa PDP. Wadannan ‘yan majalisu sun hada da wakilan kananan hukumomin Gwarzo, Gwale, Gezawa, Rogo, Madobi da Bichi. Karamin bayani a nan gaba…

Ana bincike ko cutar kyandar birrai ta je Kano

Ana bincike ko cutar kyandar birrai ta je Kano

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta ce jami’anta sun kebe wani mutum da aka ba da rahoton ya kamu da cutar kyandar birrai a jihar. A ranar Alhamis ne dai aka fara rade-radin an samu wani mutum da ya kamu da cutar, bayan tun da farko da gwamnati ta ce wani shi ma da ake […]

Sabuwar Shekarar Musulunci: Jihar Kano Ta Sanar Da Hutun Aiki Ranar Jumma’a.

Sabuwar Shekarar Musulunci: Jihar Kano Ta Sanar Da Hutun Aiki Ranar Jumma’a.

Daga Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta sanar cewa babu aiki ranar Jumma’a 22 ga watan Satumba don shaidawa da tsayawar sabuwar shekarar musulunci. Wannan na kunshe cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Malam Ibrahim Garba ya sakawa hannu ya kuma bawa manema labarai a Kano ranar Laraba. Sabuwar Shekarar Musuluncin ta dace da […]

Wani Mutum Ya Cakawa Kansa Wuka Sannan Yayi Tsalle Ya Fada Rijiya

Wani Mutum Ya Cakawa Kansa Wuka Sannan Yayi Tsalle Ya Fada Rijiya

Wani mutum mai shekaru 40 a duniya, mai suna Balarabe Adamu ya cakawa kansa wuka sannan yayi tsalle ya fada rijiya  ranar Talata a unguwar Rijiyar Zaki dake Karamar Hukumar Ungogo. Alhaji Mustapha Rilwan, Darakta a Ma’aikatar Kashe Gobara ta Jihar Kano shi ne ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa sun same ceto […]

Me Marubutan Nigeria Keyi a Lebanon?

A yanzu haka wasu marubuta goma daga sassa daban-daban na Najeriya na ziyara a kasar Lebanon a karkashin wani shiri na karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar adabi.

Me Marubutan Nigeria Keyi a Lebanon?

Marubutan na halartar tarurrukan bita suna kuma ziyartar wuraren tarihi da nufin kara fahimtar alakar da ke tsakanin al’ummun duniya ta fuskar al’adu. Gidauniyar Wole Soyinka ce ta shirya shirin da hadin gwiwar Cibiyar Cedars ta kasar Lebanon da kuma Jami’ar Notre Dame ita ma ta Lebanon. A wannan hira da ya yi da Muhammad […]

Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin sayar da takardun lamuni na Sukuk wadanda babu kudin ruwa a kansu. Hukumar da ke kula da basuka ta kasar (DMO) ce za ta kadddar da shirin, wanda aka ware kimanin naira biliyan 100. A cewar jami’ai, wannan shiri zai taimaka wurin samar da […]

An kama ‘babban kwamandan IS’ a Kano

Hukumoni a Najeriya sun ce sun kama babban kwamandan kungiyar IS reshen yankin Afirka ta yamman wanda ya kisa kai wa Musulmi hari lokacin bukukuwan babbar sallah.

An kama ‘babban kwamandan IS’ a Kano

Hukumar binciken farin kaya ta kasar (DSS) ta ce kungiyar masu tada kayar baya ta IS reshen yammacin Afirka (ISWA) ta shirya ta da zaune tsaye lokacin bukukuwan sallah wanda aka yi a makon jiya. Kungiyar ta shirya kai hare-hare a jihohin Kano da Kaduna da Neja da Bauchi da Yobe da Borno da kuma […]

Aikin Hajji: Mahajjata 2 ‘Yan Kano Sun Mutu A Saudi Arabia

Aikin Hajji: Mahajjata 2 ‘Yan Kano Sun Mutu A Saudi Arabia

Mahajjata biyu daga Jihar Kano sun rasa ransu yayin gudanar da aikin hajjin bana a Saudi Arabia, a cewar Hukumar Alhazai ta Jihar ranar Alhamis. Shugaban Sashin Hurda da Jama’a na ma’aikatar Alhaji Nuhu Badamasi ne ya sanar ta wayar tarho daga garin na Makkah cewa wadanda suka mutun duka maza ne kuma sun mutu […]