Madrid ta Lashe Kofin gasar Spanish Super Cup

Real Madrid ta lashe kofin Spanish Super Cup na bana, bayan da ta lallasa Bercelona da ci 2-0 a wasa na biyu da suka kara da daren ranar Laraba a filin wasa na Santiago Berneabue.

Madrid ta Lashe Kofin gasar Spanish Super Cup

Madrid, wadda ke rike da kambun gasar zakarrun Turai da ta Spania dai, ta kuma sha gaban Bercelona wajen murza leda a wasa duk da cewa babu Cristano Ronaldo a ciki. Marco Asensio da Karim Benzama ne suka zura wa Bercelona kwallayen biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci A zageyen farko na wasan […]