Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasar da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci, abin da ya maido da kasar cikin jerin sunayen makiyan Amurka.

Korea Ta Arewa na tallafa wa ta’addanci- Amurka

A lokacin da ya ke ayyana Korea Ta Arewa a matsayin kasa mai tallafa wa ta’addanci a fadar White House, Trump ya ce, tun da jimawa ya kamata su dauki wannan mataki. Korea Ta Arewa na ci gaba da kasancewa cikin jerin takunkuman da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka kakaba ma ta saboda gwaje-gwajenta […]

Rikicin Trump Da Korea ta Arewa ‘Ya Kai Intaha’

Shugaban Amurka Donald Trump ya sabunta gargadinsa ga Koriya ta Arewa bayan ministan wajen Korea ya yi kalamai masu zafi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Asabar.

Rikicin Trump Da Korea ta Arewa ‘Ya Kai Intaha’

Ri Yong-ho ya bayyana Mr Trump a matsayin mutum “mai tabin hankali da ke yunkurin halaka” jama’a. Shugaban na Amurka ya yi raddi ga Mr Ri da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da cewa idan suka ci gaba da barazanarsu, nan gaba kadan “za a yi ba su”. Wannan sabuwar takaddama ta taso ne […]

Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Koriya Ta Arewa na ci gaba da musayar zafafan kalamai da Amurka, inda shugaba Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mai tabin hankali.

Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa da ke birnin Pyongyang ya ambato Kim Jong-un na cewa shugaban Amurka zai yaba wa aya zaki saboda jawabin da ya yi tun farkon wannan mako a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Donald Trump ya fada wa taron cewa idan tura ta kai Amurka bango, to za ta kare […]

Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

A baya-bayan nan ne dai shugaban na Amurka ya yabawa Kim Jun-Un kan matakin daya dauke na dakatar da shirin harba wani makami mai linzami zuwa yankin Guam na Amurka

Amurka ta Sanyawa Kamfanonin Rasha da Chana Takunkumi

Kasar Amurka ta sanyawa wasu kamfanonin kasashen Rasha da Chana 16 takunkumi saboda abinda ta kira goyan bayan shirin nukiliyar kasar Koriya ta Arewa. Takunkumin na daga cikin matakan da Amurka ke dauka na dakile samun kudade ga Koriyar domin ci gaba da gina makamin. Sakataren Baitulmalin Amurka, Steven Mnuchin ya ce abin takaici ne […]

Kim Jong-un ya dakatar da kaiwa Amurka hari

Kim Jong-un ya dakatar da kaiwa Amurka hari

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya dakatar da kaiwa tsibirin Guam na kasar Amurka harin makami mai linzami a wata sanarwa da kamfanin labarai na Koriya din ya sanar. Da yake jawabi akan haka, shugaban yace zasu dakatar da kai harin har sai sun ga motsin da Amurka zata iya yi kafin su […]