Boko Haram ta kashe mutane kasuwar Konduga

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, kungiyar Boko Harm ta kaddamar da hare-haren kunar bakin wake a karamar hukumar Konduga, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27.

Boko Haram ta kashe mutane kasuwar Konduga

Maharan su tayar da bama-bamai guda biyu a wata kasuwa da ke karamar hukumar kuma a dai dai lokacin da jama’a ke tsaka da cin kasuwancinsu a yammain wannan Litinin kamar yadda wakilinmu, Bilyaminu Yusuf ya tabbatar mana. Bam na uku ya tashi ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin na Kondugan kamar […]