Fatan ’yan kasuwar Kano kan tallafin gobara

Shugaban Hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar Sabon Gari, watau Amata Alhaji Ado Bilyaminu, wanda ya nuna jin dadinsa na kaddamar da wannan asusu, inda ya bayyana cewa ‘yan kasuwar Sabon Gari masu dimbin yawa sun yi mummunar asarar dukiyoyinsu wanda sakamakon wannan gobara da yawansu ba sa zuwa kasuwa, saboda komai nasu wuta ta cinye, kuma babu wani jarin da za su iya komawa kasuwanci.

Fatan ’yan kasuwar Kano kan tallafin gobara

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani asusu domin tara kudi don  tallafa wa ‘yan kasuwar da iftila’in gobara  ya shafa,  kuma a lokuta daban-daban  a kasuwanni guda biyar da ke jihar, watau kasuwar Sabon Gari da kasuwar Kurmi da kasuwar Singa kasuwar garin Gwarzo da kuma kasuwar sayar da wayoyin hannu da ke Farm Centre. […]