‘Yan Okada Sun Fara Yajin Aiki A Jihar Legas

Masu sana'ar Okada a birnin Legas, wadanda yawancinsu daga jihohin arewa suka fito, sun shiga yajin aiki saboda a cewarsu 'yan sandan jihar na tursasa musu tare da tatsarsu kudade na ba gaira ba dalili.

‘Yan Okada Sun Fara Yajin Aiki A Jihar Legas

Masu haya da babura da aka fi sani da ‘yan Okada a birnin Legas sun fara wani yajin aiki na sai “baba ta gani” sanadiyyar matakin da rundunar ‘yan sandan jihar ta dauka na fara kam asu muddin ba su bi wasu ka’idoji ba. Rundunar ta bukace su, da su rika sanya wasu kaya da […]

Ina Hakkokin Masu Taimaka Wa EFCC Da Bayanai

Ina Hakkokin Masu Taimaka Wa EFCC Da Bayanai

A Najeriya, sama da watanni shida bayan da wasu suka tseguntawa hukumar EFCC da bayanai don gano bilyoyin kudaden da aka boye a wani gida da ke unguwar Ikoyi a birnin Lagos, har yanzu gwamnati ba ta bai wa wadanda suka taimaka da bayanai domin gano kudaden hakkokinsu na 5% da doka ta ce a […]

Wani Darakta Ya Kashe Kansa A Legas

Wani Darakta Ya Kashe Kansa A Legas

Mr Oludare Buraimoh Mai Matsayin Mukamin Darakta ne a Ma’ikatar Matasa ta Jihar Legas ya kashe kansa ta hanyar rataya a cikin dakinsa Buraimoh wanda ke zaune a rukunin gidajen Unity dake Gbonagun a Abeokuta ya kashe kansa ne da misalin karfe 4:00 na yamma ranar Litinin bayan da ya ziyarci dansa Dotun da bashi […]

Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

Nigeria za ta fara sayar da takardun lamunin Musulunci

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin sayar da takardun lamuni na Sukuk wadanda babu kudin ruwa a kansu. Hukumar da ke kula da basuka ta kasar (DMO) ce za ta kadddar da shirin, wanda aka ware kimanin naira biliyan 100. A cewar jami’ai, wannan shiri zai taimaka wurin samar da […]

An Gurfanar da Malamin Makaranta Saboda Zargisa da Lalata da ‘Yan Mata 3 ‘Yan Uwan Juna

An Gurfanar da Malamin Makaranta Saboda Zargisa da Lalata da ‘Yan Mata 3 ‘Yan Uwan Juna

Daga Garin Lagos- Wani Malamin makaranta mai shekaru 23 mai suna Ibrahim Idris ya bayyana a gaban kotun majistire  ranar Talata saboda zarginsa da lalata da ‘yan mata uku ‘yan gida daya. Wanda ake zargin malamin makaranta ne dake koyar da ilimin Arabiya na zaune a gida mai lamba 2, layin Kelani, dake tashar Adealu […]

Rikici ya barke tsakanin al’ummar Hausawa a Lagos

Rikici ya barke tsakanin al’ummar Hausawa a Lagos

Rahotannin daga jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya na cewa wani rikici ya barke a tsakanin al’ummar Hausawa da ke a babbar kasuwa ta Alabaraho. Wasu rahotanni na cewa an garzaya da mutum takwas asibiti wadanda aka raunata. Rikicin dai ya taso bayan kokarin da ake a sasanta tsakanin wasu sassa biyu da basa ga-maciji […]

Rikici ya barke tsakanin al’ummar Hausawa a Lagos

Rahotannin da mu ke samu na cewa wani mummunan rikici ya barke a tsakanin al'ummar Hausawa da ke a babbar kasuwa ta Alaba Rago.

Rikici ya barke tsakanin al’ummar Hausawa a Lagos

Wasu rahotanni na cewa an sassari mutum takwas da raunata wasu da dama. Rikicin dai ya taso bayan kokarin da ake a sasanta tsakanin wasu sassa biyu da basa ga-maciji da juna a kan wanene shugaban kasuwar Alaba rago. Tuni dai aka tura jami’an tsaro na ‘yan sanda. Za mu kawo muku karin bayani nan […]

An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Legas

Ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kawo cikas ga zaben kanana hukumomi a wasu yankunan birnin Legas.

An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Legas

A yau aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Legas kuma zaben ya tafi dai dai yadda aka tsara a wasu yankuna na birnin Legas,inda ba a samu ambaliyar ruwa ba. Rahotani na nuni da cewa jama’a sun fito sosai domin jefa kuri’arsu, amma akwai rahotani dake cewa ba a samu fitowar mutane da […]

Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya dakatar da Yusuf Ogundare, wanda shi ne basaraken Shangisha a Magodo da ke cikin jihar Legas saboda kitsa shirin sace kansa da kaninsa a matsayin garkuwa.

Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

A ranar 5 ga watan Yuli ne basaraken ya bace a cikin karamar hukumar Ikosi-Isheri ta jihar Legas. A sanadiyyar wannan ne gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya dakatar da basaraken daga aiki. A wata sanarwar da kwamishinan kananan hukumomi da al’ummomi ya sanya wa hannu, ta ce gwamnan ya dakatar da basaraken daga aikinsa. […]

Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Al'amura sun tsaya cak, yayin da mutane suka kasance a gida a wasu sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, bayan wani ruwansa da aka kwashe kwanaki ana yi ya haddasa ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Mazauna unguwannin Lekki da Victoria Island sun wari gari ranar Asabar da ambaliyar ruwa bayan kwashe kwana biyar a ruwa, kamar yadda wata wadda take zaune a Legas ta shaida wa BBC. “Yau kwana biyar ke nan ana ruwa babu dauke wa a unguwar Lekki. Ko ‘ya’yanmu ma a cikin ruwa suke zuwa makaranta cikinsa […]