Ma’aikaciyar British Airways Taci Zarafin ‘Yan Nigeria a Bidiyo

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na mallakin Birtaniya, British Airways, ya kaddamar da wani bincike kan wani bidiyo da bayyana, inda daya daga cikin ma'aikatan jiragensu ta yi wasu kalaman da ake danganta su da na nuna wariyar launin fata kan 'yan Najeriya.

Ma’aikaciyar British Airways Taci Zarafin ‘Yan Nigeria a Bidiyo

Ma’aikaciyar dai ta dauki bidiyon kanta ne a yayin da take kan hanyarta ta zuwa filin jirgi inda a ranar za ta yi aiki da jirgin da zai tafi Abuja babban birnin Najeriya daga filin jirgin sama na Heathrow da ke London. A wani sako da kamfanin BA ya aikewa BBC ya ce: “Tun bayan […]

Shugaba Buhari zai koma gida daga London

Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar ranar Lahadi bayan kammala abin da ya kai shi London.

Shugaba Buhari zai koma gida daga London

Shugaban ya tafi London ne ranar Alhamis bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Amurka. Daya daga cikin jami’an da suka raka shugaban Amurka ya tabbatarwar BBC cewa tsarin tafiye-tafiyen mai gidan nasa ya nuna cewa zai koma kasar ne ranar ta Lahadi. Kafin tafiyar tasa London, Shugaba Buhari ya gabatar […]

‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Wata 'yar jarida daga arewa maso gabashin Najeriya ce ta lashe lambar yabo ta BBC ta Komla Dumor ta bana.

‘Yar arewacin Nigeria ta ci gasar Komla Dumor ta BBC ta 2017

Amina Yuguda mai gabatar da labarai ce a gidan talbijin na Gotel da ke Yola, inda ta gabatar da labarai da dama har da wadanda suka shafi rikicin Boko Haram. Za ta fara aikin koyon sanin makamar aiki na tsawon wata uku a London cikin watan Satumba. An kirkiro lambar yabon ne don girmama Komla […]

Duba lafiyar Shugaba Buhari za a sake yi a London?

Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai je London bayan ya kammala taron majalisar dinkin duniya da za a yi a Amurka makon gobe.

Duba lafiyar Shugaba Buhari za a sake yi a London?

Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai ta ce Shugaba Buhari zai je birnin New York na Amurka ranar Lahadi, domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar Dinkin Duniya karo na 72, tare da sauran shugabannin kasashen duniya. A cewar sanarwar Shugaban “zai je birnin London a kan hanyarsa ta komawa […]

Wasu abubuwa sun fashe a tashar jirgin London

Rundunar ‘yan sandan London ta ce tana kallon harin da aka kai a wata tashar jirgin birnin a matsayin na “ta’addanci”. Wasu fasinjojin jirgin karkashin kasa na London sun ji raunuka bayan wani abu ya fashe a tashar District Line da ke kudu maso yammacin birnin. An yi kiran ‘yan sanda da likitoci da misalin […]

Shin Ya Kamata Buhari Ya Yi wa Gwamnatinsa Garambawul?

A Najeriya ana ci gaba da kiraye-kiraye kan cewa lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa gwamnatinsa kwaskwarima.

Shin Ya Kamata Buhari Ya Yi wa Gwamnatinsa Garambawul?

Batun kiraye-kiraye da ake yi na neman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a gwamnatinsa na janyo ka-ce-na-ce tun bayan da shugaban ya dawo daga jinya a London inda ya kwashe sama da watanni uku. Wannan korafi da mutane ke gabatarwa na zuwa ne yayin da gwamnatin ta APC ta kwashe sama da shekaru […]

Ban Mayar Da Osinbajo Saniyar-Ware Ba — Buhari

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce mataimakin Shugaba Buhari na nan da karfin ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, kuma ba a mayar da shi saniyar-ware ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.

Ban Mayar Da Osinbajo Saniyar-Ware Ba — Buhari

Malam Garba Shehu mai magana da yawun Shugaba Buharin ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, bayan da wata jarida ta ce tun bayan dawowar Shugaba Buhari daga jinya wasu daga cikin ‘yan fadarsa da suka yi baba-kere sun ware Farfesa Osinbajo inda ba a damawa da shi a harkokin […]

Wasu Mahajjata Tara Sun Isa Madina a Keke Daga London

Wasu mahajjatan Birtaniya su tara sun isa birnin Madinah na Saudiyya a keke, bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga London.

Wasu Mahajjata Tara Sun Isa Madina a Keke Daga London

Hukumomin Saudiyya sun tarbi mutanen a Madina cike da murna da jinjina a gare su. Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa kungioyin masu tseren kekuna na Madinah da Taibah ne suka tarbi mahajjatan karkashin jagorancin hukumar wasanni ta Saudiyya, inda aka dinga yi musu kade-kade da watsa musu furanni don […]

An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen ‘yan sanda

An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen ‘yan sanda

An kai rahoton Sarauniyar Ingila ga ‘Yan sandan West Yorkshire saboda rashin sanya maɗauri a cikin motar masarauta a kan hanyarta ta zuwa bikin buɗe zaman Majalisa. Wani mutum ne ya buga lambar kar-ta-kwana ta 999, inda ya tsegunta wa ‘yan sanda cewa Sarauniya ba ta sa bel ba a motar da ake tuƙa ta […]

Kamfanin sufuri na Uber ya mayar wa fasinjoji kudade

Kamfanin sufuri na Uber ya mayar wa fasinjoji kudade

Kamfanin Uber ya mayar wa fasinjojin da suka yi amfani da manhajar kamfanin a kusa da gadar da aka kai harin ta’addanci na birnin Landan. Kamfanin sufurin ya sha suka daga jama’a a zaurukan zumunta na intanet saboda kyale kudin mota ya tashi a lokacin harin wanda aka kai da misalin karfe 10 na dare. […]