’Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu a Adamawa

’Yan Kungiyar Boko Haram sun sake kai hari tare da kone kauyukan Muduvu da Nyibango da ke cikin Karamar Hukumar Madagali a jihar Adamawa.

’Yan Boko Haram sun kashe mutum biyu a Adamawa

’Yan Kungiyar Boko Haram sun sake kai hari tare da kone kauyukan Muduvu da Nyibango da ke cikin Karamar Hukumar Madagali a jihar Adamawa. Harin ya auku ne bayan ’yan kwanaki da kai irinsa a kauyukan Ghumbili da Mildu inda mutane da dama suka bata. Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Malam Yusuf Muhammed ya fada wa […]

‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a jihar Adamawa

‘Yan Boko Haram sun kai sabon hari a jihar Adamawa

‘Yan Boko Haram sun tura hari  a uguyoyi uku a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa. Yan ta’addar suna nema su maida Adamawa kamar yadda sukayi wa Jahar Maiduguri. Sun kai harin ne a  karamar hukumar Mildu wanda har mutane bakwai suka rasa rayukansu. Sun sake kai hari a jahohin Muduvu da Nyibango. Daga bakin  […]

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13

Rundunar Sojan Najeriya ta kashe fiye da ’yan kungiyar Boko Haram 13 a wani simamen da ta kai a sassan jihar Borno da Adamawa.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13

          Rundunar Sojan Najeriya ta kashe fiye da ’yan kungiyar Boko Haram 13 a wani simamen da ta kai a sassan jihar Borno da Adamawa. Mai Magana da Yawun Rundunar, Birgediya Ganar , Sani Usman shi ne ya tabbatar da lamarin a wata sanarwar da rundunar ta raba wa manema labarai […]

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Salon Kai Hari

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa yanzu haka mayakan Boko Haram sun sauya salo inda suke fakewa yin zaman makoki domin kai hari kamar yadda suka yiwa mutanen Madagali garin dake kusa da dajin Sambisa inda suka ja tunga.

Kungiyar Boko Haram Ta Sake Salon Kai Hari

          WASHINGTON DC —  Wannan ne dai kusan karo na uku a kasa da mako guda da yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a wasu kauyuka na yankin Madagalin dake daura da dajin Sambisa. Yayin wannan harin ,kamar yadda rahotanni ke cewa yan tada kayar bayan sun yi shigar […]

Wasu ‘Yanbindiga Sun Yiwa Mutane Yankan Rago a Midul, Adamawa

Yayinda ake zaton hare-haren ta'addanci ya ragu sai gashi a daren jiya wasu 'yanbinda da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yiwa mutane yankan rago a Midul cikin karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa

Wasu ‘Yanbindiga Sun Yiwa Mutane Yankan Rago a Midul, Adamawa

Wasu ‘yanbindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun yiwa wasu yankan rago a garin Midul dake cikin karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa Arewa maso gabashin Najeriya. Rahotanni na cewa ‘yan bindiga sun yi shigan burtu ne cikin dare inda suka farma kauyen mai tazaran kilomita ko zuwa bakwai zuwa garin […]