Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Koriya Ta Arewa na ci gaba da musayar zafafan kalamai da Amurka, inda shugaba Kim Jong-un ya bayyana Donald Trump a matsayin mai tabin hankali.

Kim Jong-un Ya Ce Trump Na Da Tabin Hankali

Kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa da ke birnin Pyongyang ya ambato Kim Jong-un na cewa shugaban Amurka zai yaba wa aya zaki saboda jawabin da ya yi tun farkon wannan mako a Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Donald Trump ya fada wa taron cewa idan tura ta kai Amurka bango, to za ta kare […]